Iran Za Ta Kaddamar Da Wasu Tauraron Dan'Adam Guda Uku
Ministan sadarwa da fasaha na kasar Iran ya sanar da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran na shirin aikawa da wasu sabbin tauraron dan'adam da masanan kasar suka kera zuwa sararin samaniyya a karshen wannan shekara ta hijira shamsiyya da ke karewa a watan Maris mai kamawa.
Ministan sadarwa da fasahar na Iran Mahmoud Vaezi ya bayyana hakan ne a watan ganawa da yayi jiya Laraba da manema labarai inda ya ce a karshen shekarar ne za a harba tauroron dan'adam din nan mai suna Sharif, kana kuma daga baya a cikin shekarar za a sake aikawa da wasu tauraron dan'adam din guda biyu na daban.
Ministan ya kara da cewa dukkanin wadannan tauraron dan'adam din guda uku masana da kwararrun matasa na Iran ne suka kera su, kamar yadda kuma ya ce a halin yanzu gwmanatin ta Iran tana kan tattaunawa da kasar Rasha kan kera wasu tauraron dan'adam din.
A shekara ta 2009 ne dai Iran ta fara kera tauraron dan'adam dinta na farko da aka ba shi sunan Omid, wato kyakkawan fata, tun daga nan kuma masanan kasar Iran din sun ci gaba da kera wasu taurarin dan'adam din da suka da Fajr wanda yake da karfin gaske wajen tattaro bayanai da kuma aiko da hotuna masu inganci. A shekara ta 2010 ne kuma Iran din ta aike da wata dabba zuwa sararin samaniyya ta hanyar amfani da na'urar da masanan kasar suka kera mai suna Kavoshgar-3.