Dakarun Iran Sun Fara Wani Gagarumin Atisayen Hadin Gwuiwa
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i15718-dakarun_iran_sun_fara_wani_gagarumin_atisayen_hadin_gwuiwa
Sojojin kasa na Iran tare da bangaren kare sararin samaniyya na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na kasar (IRGC) sun fara gudanar da wani atisaye na hadin gwuiwa a kudancin kasar ta Iran daga duk wata barazana ta makiya.
(last modified 2018-08-22T06:59:26+00:00 )
Dec 26, 2016 07:22 UTC
  • Dakarun Iran Sun Fara Wani Gagarumin Atisayen Hadin Gwuiwa

Sojojin kasa na Iran tare da bangaren kare sararin samaniyya na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na kasar (IRGC) sun fara gudanar da wani atisaye na hadin gwuiwa a kudancin kasar ta Iran daga duk wata barazana ta makiya.

Tashar talabijin din Press TV da ke watsa shirye shiryenta daga nan Tehran ta ba da rahoton cewa a safiyar yau ne dakarun bangarorin biyu na suka fara gudanar da wannan atisayen da aka ba shi sunan 'Modafe'en Asemane Velayat 7 (Wato masu kare sararin samaniyyar Wilaya na 7) wanda zai dauki kwanaki uku ana gudanar da shi.

Manufar wannan atisayen dai ita ce hadin gwuiwa da aiki tare tsakanin bangarori daban-daban na dakarun kasar ta Iran a kokarin su na kare sararin samaniyyar kasar daga dukkanin hare-haren da makiya za su iya kawo ta sama.

Ya zuwa yanzu dai an gwada dabaru daban-daban na yaki wajen kare sararin samaniyyar bugu da kari kan wasu sabbin na'urori da suka hada da na'urorin rada-rada masu karfin gaske, bugu da kari kan wasu makamai masu linzami da kuma na'urorin sadarwa da dai sauransu.