Ana Zamen Makoki Na Kwanaki Uku A Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i16315-ana_zamen_makoki_na_kwanaki_uku_a_iran
A Jamhuriya musulinci ta Iran an shiga zamen makoki na kwanaki uku bayan rasuwar tsohon shugaban kasar Ayatollah Ali Akbar Hachemi Rafsandjani.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jan 09, 2017 07:24 UTC
  • Ana Zamen Makoki Na Kwanaki Uku A Iran

A Jamhuriya musulinci ta Iran an shiga zamen makoki na kwanaki uku bayan rasuwar tsohon shugaban kasar Ayatollah Ali Akbar Hachemi Rafsandjani.

Za'a dai yi jana'izar mirigayin dan shekaru tamanin da biyu a duniya a gobe Talata a hubbaren Iman Khomaini dake birnin Teheran. 

Da yammacin jiyya ne Allah ya yiwa Rafsandjani wanda shi ne shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin muslunci ta Iran rasuwa sakamakon matsalar zuciya.

A rayuwarsa Rafsanjani ya rike shugabancin kasar Iran daga shekarar 1989 zuwa 1997.