Iran Ta Karbi Jirgin Farko Daga Kanfanin Airbus
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i16516-iran_ta_karbi_jirgin_farko_daga_kanfanin_airbus
Jamhuriya muslunci ta Iran ta sanar da karbar daya daga cikin jiragen sama kirar airbus datayo oda tun bayan yaye mata kallabin takunkumin da aka dora mata.
(last modified 2018-08-22T06:59:32+00:00 )
Jan 12, 2017 12:55 UTC
  • Iran Ta Karbi Jirgin Farko Daga Kanfanin Airbus

Jamhuriya muslunci ta Iran ta sanar da karbar daya daga cikin jiragen sama kirar airbus datayo oda tun bayan yaye mata kallabin takunkumin da aka dora mata.

Wannan dai shi ne jirgi na farko kirar airbus da Iran din ta karba cikin guda 100 data yo oda tun bayan yarjejeniyar data cimma da mayan kasahen duniya wanda ya kai ga dage mata takunkumin kasuwanci.

Ministan sufuri na kasar ta Iran ne Abbas Akhoundi, ya jagoranci karbar jirgin na farko kirar A 321 a yau Alhamis a filin sauka da tashin jiragen sama na Mehrabad dake nan Teheran, inda ya kara da cewa za'a karbi wasu biyu daga cikin jiragen kirar A 330 nan zuwa karshen shekara Iraniyawa wato wajajen 20 ga watan Maris na shekara 2017 Miladiya da kuma wasu a cikin shekara mai zuwa.

Jirgin dai ya taso ne kanfanin kera jiragen saman na Turai dake birnin Toulouse na faransa tare da Darecta manaja na sashen kasuwanci na kanfanin Airbus din, Fabrice Brégier.

A bara ne dai kanfain Iran Air ya cimma yarjejeniyar sayan jiragen sama guda 100 da kanfanin Airbus na sabar zunzutun kudi dallar Amurka Bilyan 20, bayan sanya hannu kan yarjejeniyar ta tsakanin Paris da Teheran.

ko baya ga hakan Iran ta cimma wata yarjejeniya na sayan wasu jigaren sama kirar Boeing na Amurka guda 80, wanda ya kasance na farko a kusa da shekaru 40.