Mogherini: Tarayyar Turai Zata Ci Gaba Da Mutunbta Yerjejeniya Da Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i16669-mogherini_tarayyar_turai_zata_ci_gaba_da_mutunbta_yerjejeniya_da_iran
Jami'a wacce take kula da harkokin kasashen waje na kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini, ta bayyana cewa tarayyar Turai zata ci gaba da mutunta yerjejeniyar da manya manyan kasashen duniya 5 suka cimma da iran kan shirinta na makamashin nukliya ko da kuwa gwamnatin AMurka mai kamawa ta yi watsi da ita.
(last modified 2019-03-07T05:37:59+00:00 )
Jan 16, 2017 11:51 UTC
  • Mogherini: Tarayyar Turai Zata Ci Gaba Da Mutunbta Yerjejeniya Da Iran

Jami'a wacce take kula da harkokin kasashen waje na kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini, ta bayyana cewa tarayyar Turai zata ci gaba da mutunta yerjejeniyar da manya manyan kasashen duniya 5 suka cimma da iran kan shirinta na makamashin nukliya ko da kuwa gwamnatin AMurka mai kamawa ta yi watsi da ita.

Mogherini ta bayyana haka ne a wani taron ministocin kungiyar a birnin Brussels. Jami'ar ta kara da cewa yerjejeniyar da Tehran da cimma da kasashe 5+1 tare da Iran ya nuna cewa diblomasiyya tana aiki wajen warware matsaloli, kuma ga tarayyar Turai yerjejeniyar tana a matsayin lamuni ne ga tsaron kasashen.

Kafin haka dai Donal Trump zabebben shugaban kasar Amurka ya sha nanata cewa yerjejeniyar 5+1 tare da Iran ita ce yerjejeniya mafi muni wacce Amurka ta amince da iya. Kuma zai yi watsi da ita idan ya karbi iko da kasar. 

Sai dai a dayan bangaren kuma Abbas Araqchi, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa Hukumar IAEA ta tabbatar da cewa Iran ta cika alkawuran da dauka a cikin yerjejeniyar, don haka idan shugaban Amurka mai zuwa ya yage takardun yarjejeniyar kamar yadda yake fada to kuwa Iran zata kona nata.