An Kammala Zaman Tattaunawa Kan Al'adu Tsakanin Iran Da Larabawa
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i16979-an_kammala_zaman_tattaunawa_kan_al'adu_tsakanin_iran_da_larabawa
An kammala zaman tattaunawa na farko kan al'adu tsakanin Iran da larabawa a birnin Tehran, tare da halarta masana 85 daga kasashen larabawa daba-daban.
(last modified 2018-08-22T06:59:35+00:00 )
Jan 25, 2017 04:04 UTC
  • An Kammala Zaman Tattaunawa Kan Al'adu Tsakanin Iran Da Larabawa

An kammala zaman tattaunawa na farko kan al'adu tsakanin Iran da larabawa a birnin Tehran, tare da halarta masana 85 daga kasashen larabawa daba-daban.

An fara gudanar da zaman ne a ranar Lahadi da ta gabata tare da halartar manyan jami'ai daga ma'aikatar al'adu ta kasar Iran a jami'ar Shahid Beheshti da ke Tehran.

Zaman dai ya samu halartar masana 85 daga kasashen larabawa daban-daban, da suka hada da Algeria, Tunisia, Masar, Morocco, Syria, Lebanon, Iraki, Jordan, Kuwait, Oman da sauransu.

Babban abin da zaman taron ya mayar da hankali a kansa shi ne, hanyoyin da za a bi domin kara bunkasa al'adu na muslunci a tsakanin Iran da sauran kasashen larabawa, kasantuwar cewa dukaknin al'ummomin biyu suna da tsohon tarihi wajen yin tarayya a cikin al'adu, kamar yadda kuma  addinin muslunci ya hada su a kan turba guda ta imani.

Baya ga haka kuma batun wayar da kan al'ummomi dangane da bin sahihin tunani madaidaici a cikin addini, tare da girmama fahimtar juna a dukkanin bangarori na addini ne ko na al'adu ko zamantakewa ko siyasa da dai sauransu.

Dukkanin mahalarta taron sun bayyana gamsuwarsu da yadda ya gudana, tare da bayyana cewa hakan zai taimaka matuka wajen kara hada kan al'ummomin biyu.