Ruhani:Karfin Makaman Kasar Iran Don Kare Yankin Gabas Ta Tsakiya Ne
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i17019-ruhani_karfin_makaman_kasar_iran_don_kare_yankin_gabas_ta_tsakiya_ne
Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya bayyana cewa karfin sojen da Iran take da shi na tabbatar da zaman lafiya a yanin da kuma na makobtan ta ne.
(last modified 2018-08-22T06:59:35+00:00 )
Jan 26, 2017 03:09 UTC
  • Ruhani:Karfin Makaman Kasar Iran Don Kare Yankin Gabas Ta Tsakiya Ne

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya bayyana cewa karfin sojen da Iran take da shi na tabbatar da zaman lafiya a yanin da kuma na makobtan ta ne.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacinda yake ganawa da ministan harkokin wajen kasar Kuwait Sheikh Sabah al-Khalid al-Hamad al-Sabah a nan Tehrana jiya Laraba.

Ruhuni ya kara da cewa gwamnatinsa tana goyon bayan duk wani wanda yake kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankin. Sannan zaman lafiya zata samu ne a yanikin ta hanyar tattaunawa da fahintar juna kasai. Daga karshe shugaban ya bukaci a kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu a bangarori daban daban wanda suka hada da tattalin arziki siyasa da kuma al-adu.

A nashi bangaren mnistan harkokin wajen kasar Kuwai Sheikh Sabah al-Khalid al-Hamad al-Sabah ya bayyan dalilin zuwansa Tehran don isar da sakon sarkin kasar ta Kuwaita a rubuce da shugaba Ruhani, wasikar ta kunshi jinjinawa da sarkin kasar ta Kuwait Sheikh Sabah al-Ahmad al-Jaber al-Sabah. yayiwa gwamnatin kasar Iran kan rawan da take takawa a bangaren tabbatar da zaman lafiya a yankin.