Iran Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta'addanci A Masallacin Quebec
-
Bahram Qassemi, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran
Jamhuriya Musulinci ta Iran ta yi Allah wadai da harin ta'addancin da wasu 'yan bindiga suka kai a cibiyar Islama ta birnin Quebec na kasar Canada.
Akalla mutane shida ne aka tababtar da mutuwar su yayin da wasu da dama suka jikkata lokacin da ‘yan bindiga suka bude wuta a Masallacin da ke birnin Quebec a wannan ranar Litinin.
A cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran wannan abun Allah wadarai ne kuma yana kara nuna yadda lamarin ayyukan ta'addanci bai tsaya a wannan kasa ba ko wacen ko kuma wani yanki, kalubale ne babba ga ko wace kasa.
Mista Bahram Qassemi ya kuma yi da tir da harin wanda ya danganta dana rashin imani tare da isar da juyayi ga iyalen wadanda lamarin ya rutsa dasu.
Don haka a cewarsa duniya na bukatar hadin kan kasa da kasa cikin gaggawa domin dakile yaduwar ayyukan ta'addanci.