Iran Ta Fara Atasayan Soji Da Kuma Gwajin Mayan Makamai
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i17317-iran_ta_fara_atasayan_soji_da_kuma_gwajin_mayan_makamai
Yau Asabar dakarun kare juyin juya halin musulinci na Iran sun fara wani atasayan na masamen da kuma gwajin mayan makamai.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Feb 04, 2017 07:14 UTC
  • Iran Ta Fara Atasayan Soji Da Kuma Gwajin Mayan Makamai

Yau Asabar dakarun kare juyin juya halin musulinci na Iran sun fara wani atasayan na masamen da kuma gwajin mayan makamai.

Daga cikin makaman da aka baje tare da gwadasu harda masu linzame da masu cin dogon zango da kasar ta mallaka a cewar shafin dakarun kare juyin juya halin musulinci na kasar wato Sepahnews.

Wannan atasayan na zuwa ne kwana guda bayan da sabuwar gwamnatin Amurka ta kakabawa wasu bangarori da daidaikun mutanen Iran takunkumi saboda gwajin makami mai linzamin da kasar tayi a ranar 29 ga watan Jiya.

Ana atasayen ne a yankin Semnan dake arewa maso gabashin kasar, wanda ke da niyyar nuna cewa Iran din a shirye take don tunkarar kowace irin barazana.