Iran Ta Amince Baiwa 'Yan Wasan Kokowar Amurka Visa
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i17349-iran_ta_amince_baiwa_'yan_wasan_kokowar_amurka_visa
Jamhuriya musulinci ta Iran ta amince da baiwa 'yan tawagar wasan kokowa Amurka takardar izinin shiga kasarta domin halartar gasar kokowar ta kasa da kasa.
(last modified 2018-08-22T06:59:38+00:00 )
Feb 05, 2017 07:17 UTC
  • Iran Ta Amince Baiwa 'Yan Wasan Kokowar Amurka Visa

Jamhuriya musulinci ta Iran ta amince da baiwa 'yan tawagar wasan kokowa Amurka takardar izinin shiga kasarta domin halartar gasar kokowar ta kasa da kasa.

Wannan dai na zuwa ne bayan da babbar kotun Amurka ta hana aiwatar da matakin Donald Trump na hana baki daga kasashe bakwai na musulmi shiga kasar.

Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Muhamad Javad Zarif ya bayyana a shafinsa na Tweeter cewa, zasu baiwa 'yan wasan na Amurka visa sabode soke matakin Trump da kotun Amurka ta yi.

Tunda farko dai Iran ta ce ba zata baiwa 'yan wasan na Amurkja Visa ba, a matsaytin maida martani kan matakin Trump na hana kasashen musulmi bakwai ciki har da Iran din sanya kafa cikin kasar ta Amurka.