Iran : Imam Ali Khamenei Ya Yi Watsi Da Barazana Trump
Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayatollahi Sayyid Ali Khamenei, yayi watsi da duk wata barazana ta shugaba Donald Trump na Amurka a kan kasarsa.
A cikin wani jawabinsa gaban sojojin sama kasar yau Talata, Ayatollahi Khamenei, ya ce sabon shugaban na Amurka ya nuna ainahin fuskar Amurka, wanda ya ce wannan ya nuna duk abunda muke fada a sama da shekaru 30 cewa Amurka ba 'yar goyan baya ce ba, duk ya fito fili a cikin kamfe na Donald Trump da kuma irin matakan da yake dauka a yanzu.
Ya kara da cewa, masu kunfan baki akan batun kare hakkin bil adama su ne ke daure hannun karamin yaro dan shekaru biyar.
A kwanan nan ne dai kafofin yada labarai suka nuna hoton bidiyo na wani dan karamin yaro dan shekaru biyar dan asalin kasar Iran da jami'an tsaro suka daure hannunwansa a wani filin sauka ta tashin jiragen Amurka bayan fara aiki da matakin Trump na hana baki daga kasashe bakwai na musulmi shiga kasar.