Ruhani: Karfin Sojin Kasar Iran Na Kare Kai Ne
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i17487-ruhani_karfin_sojin_kasar_iran_na_kare_kai_ne
Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya bayyana cewa karfin sojen JMI na kare kai ne kai, kasar Iran bata taba mamayar wata kasa ba kuma ba ta da niyyar yin haka a nan gaba.
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
Feb 09, 2017 16:35 UTC
  • Ruhani: Karfin Sojin Kasar Iran Na Kare Kai Ne

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya bayyana cewa karfin sojen JMI na kare kai ne kai, kasar Iran bata taba mamayar wata kasa ba kuma ba ta da niyyar yin haka a nan gaba.

Tashar television ta Presstv mai watsa shirye shiyensa da harshen turanci a nan tehran ta nakal to shugaba Ruhani yana fadar haka a yau Alhamis a lokacinda yake jawabi a gaban manya manyan baki wadanda suka hada da jami'an diblomasia na kasashen duniya dake nan birnin Tehran.

Shugaban ya kara da cewa yau shekaru 38 kenan da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran, kuma shi ne juyin juya hali mafi muhimmanci a cikin karnin da ya gabata a yankin gabas ta tsakiya da ma duniya gaba daya. amma a duk tsawon wannan lokacin kasar Iran bata mamaye wata kasa ba kuma bata da niyyan yin haka a gaba. 

Amma dangene da ci gaban da kasar take samu a bangaren kere keren makamai kuma shugaban ya bayyana cewa makaman iran gaba daya don kare kai ne, iran ba zata yi amfani da su wajen kaiwa wata kasa hari ba.

A gobe jumma'a ne ake saran miliyoyin mutanen kasar Iran zasu fito kan titunan biranen kasar don nuna goyon bayansu da kuma murnar cika shekaru 38 da samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar.