Iran Ta Lallasa Amurka A Karawar Karshe Ta Kokowar Zamani Ta 2017
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i17744-iran_ta_lallasa_amurka_a_karawar_karshe_ta_kokowar_zamani_ta_2017
Tawagar 'yan kokawar zamani ta Jamhuriya musulinci ta Iran tayi nasara dauke kofin gasar ta bana bayan da ta lallasa takwarata ta Amurka da kayi 5-3 a karawar karshe
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Feb 17, 2017 14:28 UTC
  • Iran Ta Lallasa Amurka A Karawar Karshe Ta Kokowar Zamani Ta 2017

Tawagar 'yan kokawar zamani ta Jamhuriya musulinci ta Iran tayi nasara dauke kofin gasar ta bana bayan da ta lallasa takwarata ta Amurka da kayi 5-3 a karawar karshe

Yau Juma'a ne dai aka yi karawar karsen a birnin Kermanshah dake yammacin kasar ta Iran tsakanin 'yan wasan kokowar na Amurka da Iran mai karbar bakuncin gasar ta bana.

Tunda farko dai Iran ta hana tawagar 'yan wasan na Amurka shiga kasar a matsayin maida martani ga shugaba Donald Trump akan dokarsa ta hana muslmin wasu kasashe bakwai ciki har da Iran shiga AMurka, kafin daga bisani ta amunce basu visa sobada watsi da kotun Amurka tayi da matakin na Trump

Kasar Azerbaijan ce ta samu matsayi na uku bayan da ta dauke takwararta ta Turkiyya a wasan kokowar neman matsayi na uku.