Iran Ta Yi Nasara Gwada Makamin Kariya Na S-300
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i18214-iran_ta_yi_nasara_gwada_makamin_kariya_na_s_300
Jamhuriya Musilinci ta Iran ta ce tayi nasara gwada makamin nan na Kariya hare haren sama kira kasar Rasha mai suna S-300.
(last modified 2018-08-22T06:59:46+00:00 )
Mar 04, 2017 07:10 UTC
  • Iran Ta Yi Nasara Gwada Makamin Kariya Na S-300

Jamhuriya Musilinci ta Iran ta ce tayi nasara gwada makamin nan na Kariya hare haren sama kira kasar Rasha mai suna S-300.

Gidan talabijin din kasar ta Iran ya gwada hoton bidiyon yadda aka gwada makamin, inda akayi nasara kakkabo wani makami mai linzami da kuma wani jirgi mara matuki.

Da yake bayyani a gidan talabijin din kasar babban kwamadan rundinar tsaro ta sama ta Iran Janar Farzad Esmaili, ya ce akwai ma wani makami makamancin wannan na Rasha kirar kasar Iran mai suna Bavar 373 wanda ya fi karfin S-300 wanda kasar ta Iran zata gwada shi na bada dadewa ba.

Wannan dai ya tabbatar da cewa Iran din ta soma aiki da irin wannan makamin S-300 kira kasar Rasha, a daidai lokacin da kasar ke cacar-baki da sabuwar gwamnatin Donald Trump na Amurka.