Tattaunawar Iran Da Saudiyya Kan Aikin Hajjin Bana Ta Yi Armashi
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ce ta gamsu da yadda tattaunawarta ta kasance da mahukuntan Saudiyya akan shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin bana.
Akasarin batutuwan da bangarorin keda sabani akan su an shawo kansu, saidai abun da ba za a rasa ba a cewar wakilin jagoran juyin juya halin musulunci na Iran akan aikin hajji.
A wata hira da kamfanin dilancin labaren Iran na (Isna) Ali Ghazi Askar ya ce idan har aka shawo kan sauren sabanin dake akwai to yana da yakinin cewa Iran zata tura maniyatanta a aikin hajjin bana.
Daya daga cikin sabanin dake tsakanin kasashen biyu a yanzu shi ne na biyan diyya ga iyalan Iraniyawan da suka rasa rayukansu a turmutsutsun da aka samu wajen jifan shaidan a yayin gudanar da aikin hajjin shekara 2015.
Iran dai bata aike da alhazan ta ba a hajjin bara, sakamakon turmutsutsun da ya janyo shahadar alhazai 2,300 wanda Iran din ta rasa nata alhazai 464.