Unesco Ta Yaba Da Rawar Da Mata Su ke Takawa A Iran.
Mar 06, 2017 08:33 UTC
Wakiliyar Hukumar Unesco A Tehran a ce; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sami ci gaba na azo a gani, ta fuskar karfafa mata.
Wakiliyar Hukumar Unesco A Tehran Esther Kuicsh Laroche ta ce; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sami ci gaba na azo a gani, ta fuskar karfafa mata.
Laroche ta ci gaba da cewa; Mata masana a Iran suna gudanar da ayyukansu da ya zama wajibi a yaba, domin kuwa rawar da mata za su taka wajen ci gaba wani abu ne da ya zama wajibi.
A yau litinin ne dai aka bude taron karawa juna sani a jami'ar Shahid Baheshti da ke Tehran akan mata da su ka sami ci gaba.
Tags