Iran: Sojojin Ruwa Basu Bukatar Kayan Aiki Kirar Waje.
Kwamandan sojan ruwan jamhuriyar musulunci ta Iran ya ce; Iran na ci gaba da kera makamai na zamani da zai sa ba za ta bukatu da sayo kayan aiki daga waje ba.
Kwamadan sojan ruwan Iran, Real Admiral Habibullah Sayyari, da ya ke jawabi a daren jiya litinin, ya yi ishara da ci gaban da sojan ruwa su ka samu wajen kera makamai, sannan ya ce; Kasashe kadan ne a duniya su ke iya kera makamai masu tarwatsa manya jiragen ruwa masu jigilar jiragen yaki, wanda Iran tana cikinsu.
Real Admiral Sayyari ya ci gaba da cewa: A halin da ake ciki a yanzu, kwararru Iraniyawa suna kan kera jiragen yaki masu ninkaya a cikin ruwa.
Bugu da kari Sayyari ya yi ishara da cewa a halin da ake ciki a yanzu, sojojin ruwan Iran suna a cikin yankuna daban-daban na kasa da kasa, tun daga Indiya har zuwa Somaliya, sannan ya kara da cewa; Da ace babu jiragen ruwan Iran a wadannan yankunan, to da ba a sami cikakken tsaro ba a cikin yankin.