Iran Ta Karbi Jirginta Na Biyu Wajen Kamfanin Airbus
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i18446-iran_ta_karbi_jirginta_na_biyu_wajen_kamfanin_airbus
Jamhuriya Musulinci ta Iran ta karbi jirginta na biyu daga wajen kamfanin jirgin sama na Airbus.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Mar 12, 2017 02:21 UTC
  • Iran Ta Karbi Jirginta Na Biyu Wajen Kamfanin Airbus

Jamhuriya Musulinci ta Iran ta karbi jirginta na biyu daga wajen kamfanin jirgin sama na Airbus.

A Jiya Asabar ne jirgin na biyu kirar Airbus A330-200  da kasar ta saya ya sauka a filin jirgin sama na Mehrabad dake Tehran babban birnin kasar.

Wannan dai shi ne jirgi na biyu kirar airbus da Iran din ta karba cikin guda 100 data yo odarsu tun bayan yarjejeniyar data cimma da mayan kasashen duniya wanda ya kai ga dage mata takunkumin kasuwanci.

A bara ne dai kamfanin Iran Air ya cimma yarjejeniyar sayan jiragen sama guda 100 da kanfanin Airbus na zunzutun kudade na dallar Amurka Bilyan 20, bayan sanya hannu kan yarjejeniyar ta tsakanin Paris da Teheran.

Ko baya ga yarjejeniyar sanya jiragen sama na fasinja dake tsakanin Iran da faransa da akwai wata yarjejeniyar cinikaya ta jiragen sama na Boinga guda 80 dake tsakanin Iran da Amurka. 

A shekara 2018 mai zuwa ce ake sa ran Iran zata fara karbar jiragen Boinga daga Amurka, a yarjeejniyar da suka cimma da kanfanin Boing wace ta kasance ta farko cikin shekaru 40.