Sakon Shugaba Ruhani Na Sabuwa Shekara
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i18676-sakon_shugaba_ruhani_na_sabuwa_shekara
Shugaban kasar Iran Hassan Ruhani ya taya al'ummar kasarsa murnar shiga sabuwa shekara.
(last modified 2018-08-22T11:29:50+00:00 )
Mar 20, 2017 18:50 UTC
  • Sakon Shugaba Ruhani Na Sabuwa Shekara

Shugaban kasar Iran Hassan Ruhani ya taya al'ummar kasarsa murnar shiga sabuwa shekara.

A cewar shugaba Ruhani babban fatan sabuwar shekara da aka shiga shi ne na ganin zamen lafiya da hadin kai ya samu a duk duniya.

A cikin jawabin da ya gabatar Mista Ruhani ya ce babu abu mafi bukatuwa ga duniyar nan a yanzu kamar hadin kai maimakon yakar  juna. 

Sabuwar shakarar a cewar shugaba Ruhani tana bukatar hakuri, sassauci da duk albarkar da dan Adam ke bukata bisa koyarwa ta musulunci, addini na zamen lafiya.

A daya bangare kuma shugaba ruhani ya dauko misali da yadda wasu kungiyoyin 'yan ta'adda masu ikirari da sunnan addini wanda a cewarsa suka jahilta.

A karshen jawabin nasa, Ruhani ya mika sakon murnar shiga sabuwar shekara hijira shamsiya ga takwarorinsa na kasashen Afganistan, Tadjik, Pakistan, Azerbaijan, Turkmenistan, Armeniya, Kirghiz, kazakh, India da Uzbek.