Sakon Sabuwar Shekarar Hijira Shamshiyya Na Jagoran Juyin Musulunci Na Iran.
Sakon Sabuwar Shekarar Hijira Shamshiyya Na Jagoran Juyin Musulunci Na Iran.
An karaci shekaru arba'in daga cin nasarar juyin musulunci na Iran, da hakan ke nunfin an bai wa kalubale da barazana masu yawa baya. Wasu daga cikin kalubalen da juyin musuluncin ya fuskanta, tushensa shi ne siyasar Amurka da kuma wasu gwamnatocin kasashen yammacin turai domin cutar da al'ummar Iran.
Kuma har zuwa yanzu dai wannan barazanar ba ta zo karshe ba, domin ta sake daukar wani sabon salo ta fuskar tattalin arziki.
A cikin shekaru fiye da 30, Amurka babu wani nau'in takunkumin tattalin arziki wanda bata kafawa jamhuriyar musulunci ta Iran ba. Sa dai wannan bai sauya komai ba, domin kuwa babu abinda ya karawa Iran idan ba tsayin daka da jajurcewa ba.
Sakon jagoran juyin musulunci na sabuwar shekarar shamshiyya ya sake jaddada wannan batu ne. Kokari da nuna kwazo domin duakakar al'ummar Iran ba tare da samun tsaiko ba, wanda an gan shi a fili a cikin shekarar 1395 da ta zo karshe. Kuma dukkanin duniya ta yi furuci da wannan matsayin na grima da daukakar al'ummar Iran.
Ta fuskar tsaro, Iran ta kasance mai tsaro, a daidai lokacin da kasashen da su ke makwabtanta, su ke fada da matsalolin ta'addanci da rashin tsaro.
Dacen da al'ummar Iran ta samu wajen tabbatar da tsaro, duk da matsin lamba da ta ke fuskanta ta wannan fagen, yana tabbatar da cewa yunkurin al'ummar Iran na ci gaba ba mai tsaya ba ne.
Cikakkiyar masaniyar da jagoran juyin musulunci ya ke da shi akan yakin tattalin arziki ne da makiya su ka shelanta akan Iran, ya sa a kodayaushe ya ke Magana akan wajabcin karfafa ginshikan tattalin arziki a cikin gida.
Bugu da kari, jagoran juyin ya yi ishara da wajabacin " Yunkuri da kuma aiki" da kuma " Yin gyara akan yadda ake amfani da kayan masarufi" da " rubanya himma" da kuma ( Rubanya Aiki).
Sabuwar shekarar ta 1396, jagoran ya bata sunan ta " Tattalin arziki na turjiya: da kere-kere da kuma samar da aiki."
Shakka babu, daya daga cikin hanyoyin kaiwa ga cikakken tsaro ta fuskar tattalin arziki mai dorewa, ita ce ci gaba da tsarin tattalin arziki na jajurcewa. Jagoran juyin musulunci a cikin sakon nasa na sabuwar shekara ya ambaci muhimmancin wannan batu, sannan kuma ya yi tsokaci da ci gaban da aka masu a baya, sannan kuma ya ce; a ga sakamako a kasa a cikin dukkanin fagage.
Shakka babu, duk wani rauni a fagen jajurcewar tattalin arziki, zai iya haddasa illoli, saboda da la'akari da yadda a kowace shekara ake kara samun matsin lamba.
Jagoran a cikin sakon nashi na sabuwar shekara, ya bayyana cewa; fitowar da al'ummar Iran su ka yi a ranar 22 ga watan Bahman na zagayowar cin nasarar juyin musulunci, yana a matsayin maida martani ne ga shugaban kasar Amurka, kamar kuma yadda taron da aka gabatar a ranar Kudus ya ke nuni da dabi'a da kamanni na al'ummar Iran da kuma alkiblar da su ke kallo, sannan da azama wajen cimma manufa.