Iran : Harin Amurka A Syria Kuskure Ne, Ayatollah Ali Khamenei
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i19292-iran_harin_amurka_a_syria_kuskure_ne_ayatollah_ali_khamenei
Jagoran juyin Islama na kasar Iran Ayatollah Sayyid Ali Khameni, ya bayyana cewa babban kuskure ne dubarar da Amurka ta yi na kai hari sansanin sojin Syria bisa zargin amfani da makami mai guba.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Apr 09, 2017 12:48 UTC
  • Wannan maida martani ne ga Amurka wace take ganin cewa irin harin data kai Syria tana iya kai shi a wasu kasashe ciki har da Iran.
    Wannan maida martani ne ga Amurka wace take ganin cewa irin harin data kai Syria tana iya kai shi a wasu kasashe ciki har da Iran.

Jagoran juyin Islama na kasar Iran Ayatollah Sayyid Ali Khameni, ya bayyana cewa babban kuskure ne dubarar da Amurka ta yi na kai hari sansanin sojin Syria bisa zargin amfani da makami mai guba.

Ayatollah Ali Khameni wanda ke bayyana hakan yau a yayin da yake ganawa da mayan jami'an tsaron kasar ta Iran ya ce wannan dubara ta Amurka na kai hari Syria bisa wani zargi marar tushe na cimma manufofinta babban kuskure ne.

Iran dai na goyan bayan gwamnatin Bashar Al-Assad a ci gaba da yakin da take da 'yan ta'addan Da'esh kuma tana ci gaba da Allah wadai da harin da Amurka ta kai a ranar Juma'a data gabata.

Ayatollah Khameni ya kara da cewa Jamhuriya musulinci ta Iran ba zata taba ja da baya ba a fagen daga ba, saboda wata barazanar Amurka ba.  

Wannan dai na zamen maida martani ne ga Amurka wace take ganin cewa irin harin data kai Syria tana iya kai shi a wasu kasashe ciki har da Iran.