An Kawo Karshen Gasar Alkur'ani Mai Girma
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i19870-an_kawo_karshen_gasar_alkur'ani_mai_girma
An bayyana sunayen wadanda suka samu nasara daga na farko har zuwa na uku a ko wani bangare na gasar Alkur'ani mai girma karo na 34.
(last modified 2018-08-22T11:30:01+00:00 )
Apr 27, 2017 18:15 UTC
  • An Kawo Karshen Gasar Alkur'ani Mai Girma

An bayyana sunayen wadanda suka samu nasara daga na farko har zuwa na uku a ko wani bangare na gasar Alkur'ani mai girma karo na 34.

A marecen jiya laraba ne aka gudanar da taron karshe na gasar Alkur'ani mai tsarki da ya gudana a nan birnin Tehran bisa halartar manyan malima da kuma jami'an Gwamnati, sannan kuma aka bayyana wadanda suka samu nasara a gasar daga na farko zuwa na uku, a bangaren Kira'a na manya Saeed Farvizy na kasar Iran ne ya zo na farko yayin falah zalif daga kasar Siriya ya zo na biyu sai kuma Rahamatullah Bayat daga kasar Suizilland ya zo na uku.

A bangaren gasar harda na dukkanin Alkur'ani mai girma wato hifizi na manyan mutane Musa Mu'utamidy na kasar Iran ya zo na farko sai kuma Yasir Ahmad daga kasar Siriya ke biya masa wato na biyu sai kuma Abdullahi Muhamad Adam daga kasar Sudan dake biya musu a matsayi na uku, a bagaren harda ta Matasa,Alireza Danesh daga kasar Afganistan ne ya zo na farko, Adin Shaharzad na kasar Amurka ya zo na biyu sai kuma Bashir Abubacar daga kasar Nijer ke biya musu a matsayin na uku.

A bangare 'yan Mata kuwa Atna Ali Nakiy daga kasar Iran ta zo ta farko yayin da Husaina Salisu daga Najeriya ta zo ta biyu sai kuma Sandus Saeed Sidawy daga kasar Jodan ke biya musu baya a matsayi na uku.