Sadaukarwan Da Iran Take Yi Ne Ya Hana Tarwatsewar Gabas Ta Tsakiya
Babban mai bawa Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ali Akbar Velayati ya bayyana cewa sadaukarwan da JMI ta yi ne ya hana wargajewar yankin gabas ta tsakiya ya zuwa yanzu.
Velayati ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da jaridar Al-araby Al-Jaeed ta London, ya kuma kara da cewa Iran tana aiki kud da kud da gwamnatocin kasashen Syria da Iraqi don yakar yan ta'adda, wadanda suke sun rarraba kasashen yankin. Velayati ya ce tabbatar da tsaro a yankin ya zama wajibi don rashin hakan zai shafi kawo da kowa.
Ya kuma kara da cewa kasashen yankin suna iya kare kansu da kansu ba tare da wasu kasashe sun shiga cikin al-amuransu ba, sannan iran zata kara yawan sojojinta masu bada shawara kan al-amuran yaki a kasar Syria don ganin an dawo da zaman lafiya a yankin.
Dangane da samar da tuddan mun tsira guda 8 a cikin kasar ta Syria wanda ake batunsa a taron Astana kuma , Velayati ya bayyana cewa dole ne hakan ya kasance tare da yadar gwamnatin kasar Syria.