Ayatollah Khatami: 'Yan Siyasar Iran Abokan Juna Ne Bayan Zabe
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i20744-ayatollah_khatami_'yan_siyasar_iran_abokan_juna_ne_bayan_zabe
Limamin da ya jagoranci sallar jumma'a a nan Tehran Ayatollah Ahmad Khatami ya yi kira ga yan siyasa a kasar Iran, bayan zabe da kuma bayyana wadanda suka sami nasara, da su maida kasa da ke tsakaninsu kafin zabe ya zama abota da aiki tare.
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
May 26, 2017 18:08 UTC
  • Ayatollah Khatami: 'Yan Siyasar Iran Abokan Juna Ne Bayan Zabe

Limamin da ya jagoranci sallar jumma'a a nan Tehran Ayatollah Ahmad Khatami ya yi kira ga yan siyasa a kasar Iran, bayan zabe da kuma bayyana wadanda suka sami nasara, da su maida kasa da ke tsakaninsu kafin zabe ya zama abota da aiki tare.

Ayatollah Khatimi ya yaba da yadda masu kada kuri'a miliyon 41 ko kuma kashe 73 % na suke fito zabe a ranar jumma'a da ta gabata suka zabi shugaban kasa da kuma wakilan majalisun lardunan kasar.

Limamin ya kara da cewa a kasashen Amurka da Turai yawan mutanen da suke fita zabe yana tsakanin kashi 40-50 %. ya kuma kara da cewa fitowar Iranaiyawa zabe yana nuna amincewa da tsarin musulunci da yake jagorantar kasar ne. 

A wani bangare na khudubarsa limamin ya yi maganar ziyarar da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kawo yankin gabas ta tsakiya, inda ya bayyana jawaban da shugaban yayi a kasar saudia dangane da kasar Iran kan cewa ba sabbi bane. 

A wani bangare kuma limamin ya bayyana cewa abinda ke faruwa a kasar Bahrain bayan ziyarar shugaban kasar Amurka wani alamane da cewa shugaban ya bawa sarakunan bahrain lamuni na su aikataka abinda suka ga dama da mutanen kasarsu musamman Aya. Isa Qasim wanda ya kasance shugaban mutanen kasar na gwagwarmayan neman hakkokinsu.