An Bude Baje Kolin Kur'ani Na Kasa Da Kasa A Tehran
(last modified Tue, 30 May 2017 12:30:55 GMT )
May 30, 2017 12:30 UTC
  • An Bude Baje Kolin Kur'ani Na Kasa Da Kasa  A Tehran

An bude baje kolin kur'ani mai tsarki na kasa da kasa karo na 25 a birnin Tehran na kasar Iran, tare da halartar madaba'antu na cikin gida da kuma na kasashen ketare.

Ministan ma'aikatar raya al'adun muslunci Sayyid Ridha Salihi Amiri ne ya jagoranci bude taron baje kolin a yammacin jiya a bangaren gudanar da taruka na masallacin marigayi Imam Khomenei da ke birnin Tehran.

A wannan baje kolin dai an nuna wasu daga cikin kayayyakin da suka shafi kur'ani da ake bugawa a Iran, da suka hada kwafi-kwafi na kur'ani da kuma na'urori iri-iri da suke dauke da shirye-shirye daban-daban kur'ani, da suka hada da na'urori masu kwakwalwa da sauransu.

Wannan dai shi ne karo na 25 da ake gudanar da wannan babban taro na baje kolin kur'ani mai tsarki na duniya a birnin Tehran.