Iran Na Shirin Harba wasu Taurarin Dan Adam 3 Zuwa Sararin Samaniya
Hukumar kula da harkokin bincike da ayyuka na sararin samaniya akasar Iran ta sanar da cewa, tana shirin harba wasu taurarin dan adam guda uku zuwa sararin samaniya a cikin wannan shekara.
Mataimakin shugaban hukumar Hamayun Sadr ne ya sanar da hakan a zantawarsa da manema labarai a birnin Tehran fadar mulkin kasar ta Iran, inda ya ce yanzu haka sun kammala aikin hada wadannan na'urori na tauraroon dan adam wadanda masana a kasar ta Iran suka kera, kuma nan ba da jimawa ba za a sanar da lokacin harba su zuwa sararin samaniya, domin gudanar da wasu ayyuka na musamman.
Iran dai ita ce kasar musulmi ta farko da ta fara harba tauraron dan adam zuwa sararin samaniya a cikin nasara, kuma har yanzu take ci gaba da kara fadada irin wadannan ayyuka a cikin sararin samaniya domin gudanar da bincike, da kuma ayyuka na tsaro, inda kuma ta bayyana cewa a shirye take ta taimaka ma sauran kasashen musulmi matukar dai suka nuna sha'awarsu kan hakan.