Rauhani: Azumi Jarabawa Ce Ta Allah Domin Tarbiyantar Da Ruhin Musulmi
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i20910-rauhani_azumi_jarabawa_ce_ta_allah_domin_tarbiyantar_da_ruhin_musulmi
Shugaba Hassan Rauhani na Iran bayyana ibadar azumi a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan ibada da ke a matsayin jarawa ta ubangiji ga musulmi, domin tsarkake ruhinsu a kan hakuri, tausaya wa marassa karfi, kaskantar da kai wajen bin umarnin Allah, tare da hana rai abin da yake bukata.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Jun 01, 2017 02:29 UTC
  • Rauhani: Azumi Jarabawa Ce Ta Allah Domin Tarbiyantar Da Ruhin Musulmi

Shugaba Hassan Rauhani na Iran bayyana ibadar azumi a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan ibada da ke a matsayin jarawa ta ubangiji ga musulmi, domin tsarkake ruhinsu a kan hakuri, tausaya wa marassa karfi, kaskantar da kai wajen bin umarnin Allah, tare da hana rai abin da yake bukata.

Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a daren jiya a lokacin da ya halarci wani cin abincin buda baki da aka gayyace shi a cikin Tehran.

A lokacin da yake gabatar da jawabi a wurin, shugaba Rauhani ya bayyana cewa, Allah ya wajabta azumi a kan musulmi ne domin su samu kamala ta tsoron Allah, wadda ita ce mabudin samun dukkanin rabo na duniya da lahira.

A jiya ne kwamitin kare kundin tsarin mulki a Iran ya tabbatar da zaben da aka yi wa shugaba Rauhani, inda ya lashe fiye kashi 58 cikin dari na dukkanin kuri'un da aka kada a lokacin zaben.