An Gudanar Da Jana'izar Shahidan Harin Ta'addanci Na Birnin Tehran
Jim kadan bayan kammala sallar Juma'a ne aka gudanar da Jana'izar Shahidan harin ta'addancin da aka kawo birnin Tehran ranar Larabar da ta gabata tare da halartar duban mutane gami da manyar jami'an gwamnatin Jamhuriyar musulunci ta Iran
Kafin hakan dai a Safiyar Yau Juma'a ne aka gudanar da taron addu'a ga Shahidan a Majalisar Shawarar musulincin ta kasar Iran tare da halartar Shugaban Kasar Dr Hasan Rohani, Shugaban Majalisar Dr Ali Larijani da kuma Shugaban bangaren shari'ar kasar Ayatollahi Sadik Amoly Larijani.
Bayan gudanar da taron Addu'o'in, an bisne Shahidan a kusa da Shahidan kare Harami dake makabartar Behesht Zahra a nan birnin Tehran
A safiyar ranar Larabar da ta gabata ce mayakan kungiyar ISIS suka kai harin ta'addanci kan Majalisar Shawarar musulinci ta kasar Iran da kuma Haramin Imam Khomeini(Q) dake nan birnin Tehran, lamarin da ya yi sanadiyar Shahadar Mutane 17 tare da jikkata wasu 52 na daban.