Ana Gudanar Da Tarukan Tunawa Da Shahadar Imam Ali (AS) A Iran
A yau ana gudanar da tarukan tunawa da zagayowar lokacin shahadar Imam Ali (AS) a fadin kasar Iran, inda irin wannan taro da aka gudanar a Husainiyar Imam Khomeini (RA) ya samu halartar jagoran juyin juya halin Islama.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a yau an gudanar da taron na tunawa da shahadar Amirul muminin Ali (AS) a Husainiyar Imam Khomeini (RA) ne tare da halartar malamai da kuma jama'a daga sassa na birnin Tehran.
An gabatar da jawabi a kan rayuwar Imam Ali (AS) musamman kwanakinsa na karshe, da kuma bayyana abubuwa da suke a matsayin darasi ga dukkanin musulmi daga rayuwarsa mai albarka.
Baya ga Tehran a sauran sassa na kasar Iran ana ci gaba da gudanar da irin wadannan taruka, a kasashen duniya daban-daban ma ana gudanar da wadannan taruka, domin tunawa da rayuwarsa mai albarka da kuma yin koyi da ayyukansa.