Shugaba Rauhani: Fitowar Miliyoyin Al'umma A Ranar Quds Jawabi Ne Ga Amurka
Shugaba Rauhani na kasar Iran ya bayyana fitowar miliyoyin al'ummar kasar Iran a ranar Qods ta duniya da cewa jawabi ne ga Amurka, a kan cewa al'ummar kasar ba a shirye suke su mika wuya ga bakaken manufofin ma'abota girman kai ba.
Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labaraia lokacin da ake gudanar da jerin gwanon ranar Quds ta duniya a birnin Tehran.
Ya ce ko shakka babu Amurka tana zaton cewa ta hanyar matsin lamba da saka takumkumai za ta iya tilasta Iran da al'ummarta su mika wuya ga bakaken manufofinta, amma kuma a kowane lokaci al'ummar Iran tana bayar da jawabi a aikace ne ga Amurka.
Rauhani ya ce lokacin mulkin mallaka ya wuce, goyon bayan da Amurka take baiwa Isra'ila maras iyaka da kuma 'yan ta'adda da suka kirkiro domin hargitsa yankin gabas ta tsakiya, duk hakan ba zai taba mayar da Isra'ila halastacciyar kasa ba, ko da kuwa wasu daga cikin kasashen yankin sun mika wuya ga bakaken manufofin Amurka da na Isra'ila.