Jagora:Yaki Da 'Yan Sahyuniya Wajibi Ne Ga Dukkanin Musulmi
(last modified Mon, 26 Jun 2017 19:08:16 GMT )
Jun 26, 2017 19:08 UTC
  • Jagora:Yaki Da 'Yan Sahyuniya Wajibi Ne Ga Dukkanin Musulmi

Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyid Aliyul Khamenei ya bayyana cewa bisa shara'ar Addinin musulinci, domin kalubalantar mamaye maƙiya ga kasar musulmi, wajibi ne ga ko wani musulimi ya yi gwagwarmaya domin haka yaki da Haramtacciyar kasar Isra'ila ya zama wajibi ga ko wani musulmi.

A yayin da yake ganawa da Jami'an Gwamnati kasar  gami da wakilan da jakadodi na kasashen waje yayin da suka je masa barka da salla a wannan rana ta Litinin, Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyid Aliyul Khamenei ya bayyana cewa Duniyar musulinci na bukatar hadin kai mai karfi, mafi yawan musulmin Duniya suna jin zafi da takaici a kan abinda yake faruwa da 'yan uwan su musulmi, domin haka ya zama wajibi ga Gwamnatoci suyi abin da ya kamata. 

Yayin da yake mayar da martani a kan wasu shugabanin kasashen musulmi kan cin kafa da kuma zarkin da suke yiwa Gwamnatin Iran a kan gwagwarmayar da take yi da Mahukunta Sahawuya, Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyid Aliyul Khamenei ya ce a halin da ake ciki ya zama wajibi ga Al'ummar musulimi su yakiHaramtacciyar kasar Isra'ila a kan mamayar da take yiwa kasar musulmi 

Jagora ya kara da cewa fitowar milyoyin Al'ummar Iran a ranar Qudus ta Duniya domin nuna goyon baya ga Al'ummar Palastinu na daga cikin Abubuwar dake sanya alfahari ga hadin kan musulmi, ma'anar hadin kai musulmi shi ne milyoyin mabiya mazhabar Shi'a na kasar Iran da Duniya  dauke da azumi su fito domin nuna goyon baya su ga 'yan uwan su mabiya mazhabar Sunna Palastinawa.