Tarihin Shahararriyar Masaniyar Lissafi Ta Duniya, Maryam Mirzakhani Ta Iran
An haifi Maryam Mirzakhani ne a ranar 3 ga watan Mayu na shekara 1977 a birnin Teheran na Iran.
Mirzakhani ta yi kararu a makarantar gaba da sakadari ta Farzanegan dake birnin Tehran, wacce makaranta ce ta 'yan mata mafi hazaka.
A shekara 1994 ta lashe lambar yabo ta duniya kan lisafi a Hong Kong, da kuma ta shekara 1995 a Toronto inda ta samu sakamako mai kyau.
Ta samu digiri na BSc a fannin lisafi a shekara 1999 a jami'ar fusaha ta Sharif dake birnin Teheran.
A lokacin da take yarinya Maryam Mirzakhani ta yi sha'awar zama marubuciyya, saidai a makarantar kwaleji lissafi ya rinjayi iliminta har tsawan rayiwa.
Ta maida kimiyar lissafi tamakar wassani, tana warware ko wane irin lissafi hatta mafi tsarkakiya.
Mirzakhani, ta bar kasarta Iran inda ta koma karatu a jami'ar Harvard ta Amurka, ta samu digiri na uku a fannin lisafi a shekara 2004 wanda jagororin jami'ar suka danganta da wanda basu taba ganin irinsa ba tsakanin daliban lissafi.
Baya ga hakan Mirzakhani ta koma koyarwa a jami'ar Princeton kafin daga bisani ta koma ta Stanford duka dai a Amurkar.
Maryam Mirzakhani ta kasance a yau macce ta farko data yi nasara samun lambar yabo ta Fields, dake da matsayin kyautar Nobel wacce ake baiwa shahararu kan lissafi 'yan kasa da shekara 40.
A lokacin da ake mika mata wannan kyautar majalisar kasa da kasa ta masana lissafi ta (ICM) ta bayyana Mirzakhani, a matsayin wata masaniya ta lisasfi da babu tamakarta saboda kwarewa wajen warwarewa da kuma hada fasaha da dabaru da tsananin kwankwanto wajen warware lissafi.
Ita ma dai a lokacin karbar kautar ta ce'' wannan babban farin ciki ne kuma zan fi yin farin ciki idan hakan zai kara zabura da diya mata na faniin kimiya da lissfi, kuma na yi ammanar cewa nan da shekaru masu zuwa ma wasu mata zasu samu irin wannan kautar''
Shahararriyar masaniyar lissafi a duniya 'yar kasar ta Iran Maryam Mirzakhani ta rasu a jiya Asabar 15 ga watan Yuli 2017 a Amurka tana mai shekara 40 a duniya.
Ita ce mace ta farko da ta taba samun kyautar Nobel kan ilimin lissafi, ta rasu bayan ta yi fama da cutar sankara a Amurka inda take da zama.
Duniya ta nuna alhini akan rashin matar, jami'ar Stanford ta ce Mirzakhani ta rasu aman ta bar tarihi da kuma ababen da yewa da ba za'a taba mantawa dasu ba, musamen ilimin kimiya da lisafi data baiwa dubban mata.
A Jamhuriya musulinci ta Iran shugaban kasar Hassan Rohani ya nuna alhini dangane da rishin matar da ya bayyanata shaharariya a fannin kimiya, wacce kuma ta haskaka sunan Iran a fannin kimiya a duniya.
Kana kuma ya ce daya take daga cikin misalai na hazikan mata da matasan Iran wadanda a koda yaushe suke son ci gaba.
Shi kuwa a nasa bangare ministan harkokin wajen kasarta Iran Muhammad Javad Zarif ya bayyana a shafinsa na Instagram ta'aziya dangane rasuwar matar.
Ko bayan ga mayan jami'an kasar dayewa daga cikin Iraniyawa a ciki da wajen kasar sun nuna alhini dangane da rasuwar.
Maryam Mirzakhani, ta rasu ta bar yarinya guda.