Larijani: Iran Ta Riga Ta Shirya Fuskantar Duk Wani Takunkumi Na Amurka
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Ali Larijani ya sheda cewa, tuni Iran ta shirya fuskantar duk wasu sabbin takunkumai na sabuwar gwamnatin Amurka.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya a garin Gonabad na kasar Iran, shugaban majalisar dokokin kasar Ali Larijani ya bayyana cewa, babbar manufar Amurka ita ce tsorata masu saka hannayen daga kasashen ketare zuwa Iran, da nufin cutar da tattalin arzikin kasar ta Iran ta wannan fuska, Larijani ya ce tuni sun shirya fuskantar hakan ta hanyar daukar wasu matakan na daban.
Shugaban majalisar dokokin kasar ta Iran ya ci gaba da cewa, takunkumin Amurka a kan Iran ba sabon lamari ba ne ga Iran dama al'ummar kasar, ya ce dukaknin ci gaban da Iran ta samu a dukkanin bangarori na ci gaban ilimi da fasahar kere-kere, duk hakan ya faru ne a karkashin takunkumin Amurka.
Haka nan kuma ya yi ishara da cewa Iran ba ta taba yin kasa a gwiwa wajen yaki da 'yan ta'adda a yankin gabas ta tsakiya ba, ko da kuwa hakan ba zai yi wa Amurka da kawayenta na yankin dadi ba.