Iran : Ana Daf da rantsar Da Shugaba Rohani
A wani lokaci idan an jima ne ake sa ran zababen shugaban Jamhuriya muslinci ta Iran, Hassan Rohani zai yi rantsuwa kama aiki a wa'addin mulkinsa na biyu.
Dokta Rohani, zai yi rantsuwar kama aiki a gaban majalisar dokokin kasar, a matsayinsa na shugaban kasar Iran na 12.
Shuwagabanni da wakilan gwamnatocin kasashe da dama ne suka halarci bikin a birnin Tehran, daga cikinsu kuwa har da shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe.
Sauren wakilan kasashen sun hada dana koriya ta Arewa, Irlande, Croatia, Hongrie, Lithuania, Portugal, Malaisia, Uganda, Saliyo, Tanzania, Swaziland Namibiya da dai saurensu, da kuma babbar jami'ar diflomatsiyar kungiyar kasashen turai a daya bangare.
A watan Mayu da ya gabata ne Hassan Rohani ya lashe zaben shugabancin kasar ta Iran da kashi 57% na yawan kuri'un da aka kada.