Majalisar Dokokin Iran Ta Fara Tantance Ministocin Rohani
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i23200-majalisar_dokokin_iran_ta_fara_tantance_ministocin_rohani
Yau Talata, majalisar dokokin Iran ta fara zaman tantance jerin sunayen ministonin da zababen shugaban kasar Hassan Rohani ya gababar mata domin nada su a sabuwar gwamnatinsa.
(last modified 2018-08-22T11:30:32+00:00 )
Aug 15, 2017 06:32 UTC
  • Majalisar Dokokin Iran Ta Fara Tantance Ministocin Rohani

Yau Talata, majalisar dokokin Iran ta fara zaman tantance jerin sunayen ministonin da zababen shugaban kasar Hassan Rohani ya gababar mata domin nada su a sabuwar gwamnatinsa.

A ranar Talata data gabata ne Shugaba Rohani ya gabatar da sunayen mambobi 17 daga cikin 18 na sabuwar gwamnatinsa ga majalisar.

A bisa doka, ko wanne minista da shugaban kasar ya gababar sai ya samu amuncewar majalisar.

Tuni dai shugaban kasar Hassan Rohani ya fara jawabi a majalisar inda zai kare jerin sunayen mutanen da ya gabatar domin nada su ministoci.

Goma daga cikin ministocin da Dr Rohani ya gabatar sun kasance na tsohuwar gwamnatinsa ne da suka hada da Mohammad Javad Zarif ministan harkokin waje, dana cikin gida Abdoreza Rahlani Fazli, da kuma na makamasi da ma'adinai Seyed Abbas Salehi.

A watan Mayu da ya gabata ne Hassan Rohani ya lashe zaben shugaban kasar Iran da kashi 57% na yawan kuri'un da aka kada.