Ganawar Jagora Da 'Yan Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran
(last modified Wed, 03 Feb 2016 18:57:10 GMT )
Feb 03, 2016 18:57 UTC
  • Ganawar Jagora Da 'Yan Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa; Yin riko da koyarwar addinin Musulunci da fada da zaluncin manyan kasashen masu girman kai da kuma kare hakkokin Palasdinawa da ake zalunta suna daga cikin manyan manufofin da Juyin Juya Halin Musulunci a Iran ya ginu a kai.

A ganawarsa da babban sakataren Majalisar kolin tsaron kasar Iran Ali Shamkhani da tawagarsa a yau Laraba: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamene’i ya jaddada cewa; Daga cikin wasiyar da Imam Khomeini {r.a} ya gabatar kuma aka kafa tubalin Juyin Juya Halin Musulunci a kansu a Iran akwai batun kasancewar Iran yantacciyar kasa, kula da matsalolin al’umma, yin riko da koyarwar addinin Musulunci, fada da kasashen masu girman kai, kare hakkokin Palasdinawa da duk wani mai rauni a duniya da kuma fada da talauci.

Har ila yau Ayatullahi Khamene’i ya jaddada batun tsaron kasa a matsayin babbar bukatar al’umma kuma tsaron kasa ya hada da karfin soji, tabbatar da tsaron kasa, karfin tattalin arziki, yancin siyasa da al’adu, kyakkyawar zamantakewa da watsuwar kyawawan dabi’un kirki a tsakanin al’umma.