Iran : Martanin Janar Firouzabadi Ga Nikki Haley
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i23600-iran_martanin_janar_firouzabadi_ga_nikki_haley
Babban hafson sojin Iran, Janar Firouzabadi ya bayyana cewa babu wata hukuma a yankin ko kuma daga wata kasa ta ketare ko da ta soji ce, da take da hurimin ziyartar cibiyoyin soji na kasar ta Iran, ba tare da amuncewar jagoran juyin juya halin musulinci na kasar ba.
(last modified 2018-08-22T11:30:36+00:00 )
Aug 28, 2017 05:50 UTC
  • Iran : Martanin Janar Firouzabadi Ga Nikki Haley

Babban hafson sojin Iran, Janar Firouzabadi ya bayyana cewa babu wata hukuma a yankin ko kuma daga wata kasa ta ketare ko da ta soji ce, da take da hurimin ziyartar cibiyoyin soji na kasar ta Iran, ba tare da amuncewar jagoran juyin juya halin musulinci na kasar ba.

Janar Firouzabadi, na maida martani ne ga kan furicin da wasu kasashen yamma musamen Amurka ke yi na tunanin cewa Iran ta bude kofofinta barikin sojinta ga masu sanya ido na kasa da kasa.

Haka zalika wannan kallamen na Janar Firouzabadi martani ne ga wakiliyar Amurka a MDD, Nikki Haley, wacce ya ce karyata duk wani tunaninta na cewa baiwa masu sanya ido na kasa da kasa damar ziyartar cibiyoyin sojin na Iran na daga cikin yarjejeniyar nukiliya da  Iran din ta cimma da kasashen duniya.

Janar Firouzabadi ya kara da cewa yarjejeniyar da aka cimma da mayan kasashen duniya kan shirin nukiliya na Iran ba tada tanadi binciken cibiyoyin soji na Iran ba, wanda ya ce wani yunkuri na Amurka kamar yadda ta saba na neman tada fitina.