Ayatullah Shahrudi: Kungiyar Da'esh Makamin Yakar Musulmi Ne A Hannun Amurka.
(last modified Fri, 01 Sep 2017 19:19:38 GMT )
Sep 01, 2017 19:19 UTC
  • Ayatullah Shahrudi: Kungiyar Da'esh Makamin Yakar Musulmi Ne A Hannun Amurka.

Shugaban majalisar fayyace maslahar musulunci ta Iran Ayatullah Mahumud Hashimi Shahrudi ya ci gaba da cewa Amurkan tana amfani da kungiyar 'yan ta'addar ta Da'esh ne domin kawar da yunkurin musulunci.

Ayatullah Shahduri ya kuma yi kira ga kasashen musulmi da su kalubalanci kungiyoyin da su ke kafirta musulmi da makircin Amurka da kuma masu haddasa sabani na mazhaba da kabilanci.

Shugaban Majalsar fayyace maslahar tsarin musuluncin na Iran ya bayyana haka ne  a yayin da yake ganawa da mataimakin shugaban kasar Iraki, Nurul Maliki.

A nashi gefen Nurul Maliki ya jinjinawa Iran saboda rawar da take takawa wajen bunkasar kasar Iraki ta tattalin arziki da siyasa, haka nan kuma taimakon da ta yi wajen yanto da yankunan kasar da hannun yan ta'adda.