Iran Na Fatan Bunkasa Shirin Makamanta Masu Linzami
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i23721-iran_na_fatan_bunkasa_shirin_makamanta_masu_linzami
Iran ta ce babban abunda ke gabanta shi ne fadada shirinta na kera makamai masu linzami da kuma fitar da makamai zuwa ga kasashe aminnanta.
(last modified 2018-08-22T07:00:38+00:00 )
Sep 03, 2017 02:00 UTC
  • Iran Na Fatan Bunkasa Shirin Makamanta Masu Linzami

Iran ta ce babban abunda ke gabanta shi ne fadada shirinta na kera makamai masu linzami da kuma fitar da makamai zuwa ga kasashe aminnanta.

Sabon ministan tsaron kasar Janar Amir Hatami ya ce kasarsa na da wani sabon shiri na ci gaba da kera makamai masu linzami, a cewar kamfanin dillancin labaren ISNA na kasar ta Iran.

Ministan ya kara da cewa Iran na kuma neman fitar da makamai waje don kaucewa yaki, saboda a cewarsa a koda yaushe idan wata kasa ta samu rauni, lokacin ne wasu ke kokarin kai mata hari, don haka a cewarsa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso to zamu isar da makamai don karfafa tsaro a yankin.

Wadannan kalaman na sabon minitsan tsaron kasar ta Iran na zuwa ne a daidai lokacin da cacar baki ke kara zafafa tsakanin mahukuntan Washigton da na Tehran.

Ko a kwanakin baya ma majalisar dokokin Iran ta amince da shirin kara yawan kudaden da ake ware wa shirin makamanta masu cin dogon zango.