Iran Na Shirin Aikewa Da Tallafi Ga Musulmin Rohingya
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i23807-iran_na_shirin_aikewa_da_tallafi_ga_musulmin_rohingya
Kungiyar agaji ta red-Crescent a Iran ta ce tana shirin aikewa da kayan tallafin abunci ga musulmin Rohingya da suka tserewa cin zarafin da jami'an tsaron Myammar ke musu.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Sep 07, 2017 11:08 UTC
  • Iran Na Shirin Aikewa Da Tallafi Ga Musulmin Rohingya

Kungiyar agaji ta red-Crescent a Iran ta ce tana shirin aikewa da kayan tallafin abunci ga musulmin Rohingya da suka tserewa cin zarafin da jami'an tsaron Myammar ke musu.

Tallafin dai ya kunshi kayan abunci da na bukatar yau da kulun wanda tuni aka shirya aikesu zuwa kasar ta Birma kamar shugaban hukumar Morteza Salimi ya sanar.

kamfanin dilancin labaren ISNA na kasar ta Iran wanda ya rawaito labarin ya ce tallafin za'a aike shi ne har zuwa kasar ta Myamar idan aka samu izinin hakan, wannan kuwa bisa umurnin shugaban kasar Hassan Rohani.

A cewar MDD, sama da 'yan musulmin Rohingya 160,000 ne suka yi gudun hijira zuwa kasar Bangaladash.

Dama kafin hakan jakadan kasar Iran a MDD, Gholam Ali Khoshrou ya samu tattaunawa da wasu kasashen musulmi kan yadda za'a tattauna batun 'yan Rohingya a zauren MDD.