Amurka Na Ci Gaba Da Zargin Iran Da Karya Yarjejeniyar Nukiliya
A yayin da lokacin bayyana matsayar gwamnatin Amurka game da yarjejjeniyar da kasar Iran ta cimma tare da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyarta na zaman lafiya ke kara kuratowa, mahukuntan na Amurka na ci gaba da kara kaimi wajen sukar Iran.
Rex Tilerson, saktaren harakokin wajen kasar Amurka yayi da'awar cewa jamhuriyar musulinci ta Iran ke dagula harakokin tsaro a yankin yammacin Asiya, duk da cewa jami'in bai gabatar da wani dalili ba, ya ce kasar Iran na jagorantar kunigoyoyin 'yan ta'adda a yankin gabas ta tsakiya, a bangare guda kuma Nicky Haley wakiliyar Amurka a MDD ta yi alkawarin cewa bayan kawo karshen 'yan ta'addar ISIS a kasar Siriya , kasar Iran ba za ta samu wuri a kasar ba.
Wadannan bayanai na zuwa ne a yayin da mahukuntan kasar Amurka ke kokarin samar da wani uziri da zai bada damar yin fatali da yarjejeniyar da manyan kasashen biyar gami da kasar Jamus suka cimma game da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.
A cikin watanin da suka gabata, mahukuntan kasar Amurka sun yi da'awar cewa Jamhuriyar musulinci ta Iran na gudanar da wani shiri dake dagula harkokin tsaro a yankin yammacin Asiya, domin haka, Iran din ta karya yarjejeniyar nukiliyar zaman lafiya da ta cimma tare da manyan kasashe 5+1, duk da cewa wannan yarjejeniya ta mayar da hankali ne kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, sannan ba ta da alaka game da abinda ya shafi harakokin siyasa da tsaron yankin yammacin Asiya.
A irin wannan yanayi mahukuntan kasar Amurka na kokarin shafawa Iran kashin kaji ne, ta yadda suke bayyana Iran din a matsayin kasa da ya kamata aji tsoronta a yankin, sannan kuma suna zargin Iran din da yin amfani da yarjejeniyar wajen kara samun karfi da gindin zama a yankin yammacin Asiya, da wannan dalili Mr Tilerson ke bayyana Iran din a matsayin kasar dake goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi a yankin.
To sai dai kungiyoyin da Mr Tilerson ke magana kan su, su ne sahun gaba wajen yakar 'yan ta'addan ISIS da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda a kasashen Siriya da Iraki.
Dangane da wannan batu, wasu masu sharhi kan harakokin tsaro da wasu kafafen yada Labaran yamma ke cewa da kungiyoyin gwagwarmaya kamar Hizbullah da Hashadu-Sha'abi ba su kasashen tare da Sojojin kasashen Iraki da Siriya ba wajen yakar 'yan ta'adda, da tsarkake yankunan dake karkashin mamayar 'yan ta'addar ISIS musaman buranan Takrit, Mausil, da halab da bai tabbatu ba.
ko da yake a bayyane yake canjin da aka samu cikin shekarun biyu na baya-bayan nan ya dagulawa mahukuntan Amurka tsarin da suka yi a yankin yammacin Asiya, da ba don kasar Iran ta bayar da gudumuwarta wajen yaki da 'yan ta'adda a yankin ba, da har yanzu wasu daga cikin garuruwa a yankin na karkashin mamayar 'yan ta'addar ISIS.
Don haka mahukuntan Amurka ke kokarin daidaita matsayin su na gwagwarmaya da kungiyoyin 'yan ta'adda wajen bayyana Jamhuriyar musulinci ta Iran a matsayin wacce ta dagula harakokin tsaro a yankin yammacin Asiya, wanda kuma da wannan uzuri ne ta kiran Iran din a matsayin wacce ta karya yarjejeniyar da ta cimma tare da manyan kasashen Duniya.