An Fara Bukukuwan Makon Kare Kai A Iran
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i24253-an_fara_bukukuwan_makon_kare_kai_a_iran
A yau 31 ga watan shahrivar wacce ta yi dai dai da 22 ga watan Satumba ne aka fara bukukuwan makon kare kai a nan Iran don tunawa da ranar da gwamnatin kasar Iraqi ta farwa kasar Iran da yaki a shekara ta 1980 da nufin kifar da Jiririyar gwamnatin musulunci a kasar.
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
Sep 22, 2017 04:20 UTC
  • An Fara Bukukuwan Makon Kare Kai A Iran

A yau 31 ga watan shahrivar wacce ta yi dai dai da 22 ga watan Satumba ne aka fara bukukuwan makon kare kai a nan Iran don tunawa da ranar da gwamnatin kasar Iraqi ta farwa kasar Iran da yaki a shekara ta 1980 da nufin kifar da Jiririyar gwamnatin musulunci a kasar.

A lokacin dai, wato shekaru 37 da suka gabata Shugaban kasar Iraqi na lokacin Sadam Husai  ya ce a cikin mako guda zai kwace iko a kasar Iran har da birnin birnin kasar Tehran, ya kuma kawo karshen juyin juya halin musulunci wanda bai dade da kafa gwamnati a kasar ba.

A lokacin dai Sadam ya na ganin tallafi da goyon bayan  da yake samu daga manya manyan kasashen duniya da kuma na  wasu kasashe larabawa, musamman  na yankin, zai  cimma burinsa kamar yadda ya tsara.

Amma tseyuwar daka wanda mutanen kasar Iran masu kishin addini suka yi ya tsawaita wannan yakin har zuwa shekaru 8 ba tare da sadam Husain ya sami nasara ba. 

A cikin wannan makon dai, kamar yadda aka saba a  ko wace shekara akan gudanar da bukukuwa daban daban don tunawa da shekarun yakin da kuma nasarorin da mutanen kasar suka samu kan makiyansu. Daga ciki akwai faretin baje kolin sabbi da tsoffin makamai wadanda  JMI ta samar da kuma wasannin sojoji daban daban.