Iran Za Ta Ci Gaba Da Karfafa Aikin Sojinta_Rohani
-
Sabon makami mai linzami da akayi wa lakabi da \\\\\\\'\\\\\\\'Khoramshahr\\\\\\\'\\\\\\\' mai cin matsakaicin zango wanda ke iya kai wa nisan kilomita 2,000
Shugaban Jamhuriya Musulinci ta Iran Hassan Rohani ya jaddada cewa kasarsa za ta ci gaba da karkafa aikin sojinta a dukkan fannoni ciki har da na makamai masu linzami.
Babbar manufar wannan a cewar shugaba Rohani, shi ne daidaita sahu da sauren kasashen yankin irinsu Isra'ila da Saudiyya wadanda ke kashe bilyoyin daloli don sayen makamai daga kasashen yamma musamen Amurka.
Dr Rohani na bayyana hakan ne a yayin faretin sojojin kasar a nan Tehran, wanda ake kira da ''makon kare kai'' wanda ake gudanarwa a zagayowar ranar kaddamar da yakin Iran-Irak a shekara 1980.
Kazalika Rohahi ya ce Iran zata karfafa aikin sojinta a kasa da sama dana ruwa, da kara karfinta a yankin, wannan kuma ba tare da neman izinin wata kasa a duniya ba, sannan za ta ci gaba da tallafawa kasashen da ake zalinta kamar Palasdinu da Yemen.
A yayin faretin, dakarun Iran sun gabatar da wani sabon makami mai linzami da akayi wa lakabi da ''Khoramshahr'' mai cin matsakaicin zango wanda ke iya kai wa nisan kilomita 2,000 kuma makamin za'a iya goya masa wasu makamai.
Hukumomin Iran sun sanar da cewa suna da karfin fasaha da zasu iya kara karfin makaman wandanda a yanzu aka takaitasu saitinsu a kilomita 2,000 aman a cewarsu ba'ayi su ba don goya masu makaman nukiliya ba.