Ministan Tsaron Iran: Iran Ba Ta Bukatar Izinin Wani Wajen Karfafa Tsaronta
Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Amir Hatami ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta bukatar neman izinin wata kasa a duniyar nan wajen karfafa tsaron kasarta.
Ministan tsaron kasar ta Iran ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a yau din nan Asabar don tunawa da zagayowar Makon Tsaron Kasa don tunawa da zagayowar kallafaffen yakin da tsohuwar gwamnatin Iraki ta kallafa wa Iran din inda ya ce: Matukar dai akwai bukata, to kuwa Iran za ta ci gaba da karfafa karfin da take da shi na tsaron kanta, yana mai cewa: Iran ba za ta taba neman izinin wata kasa ba don kera nau'oi daban-daban na makamai masu linzami da makaman kare sararin samaniyyar kasar.
Janar Hatami ya kara da cewa: Tsare-tsare da dabarun tsaron da Iran take dauka suna yin daidai ne da irin barazanar da take fuskanta. Don haka ya ce dakarun kasar za su ci gaba da kera dukkanin makaman da suke bukata wajen kare kasar daga duk wata barazana.
Kafin hakan ma dai shugaban kasar Iran din Hasan Ruhani ya bayyana cewar dakarun kasar Iran za su ci gaba da kera makamai masu linzaminsu gwargwadon yadda suke bukata, a matsayin mayar da martani da kalaman shugaban Amurka Donald Trump wanda ya zargi Iran din da kera abin da ya kira 'makamai masu hatsarin gaske' da kiranta da ta dakatar da hakan.