Iran : Babu Zancen Sake Tattauna Yarjejeniyar Nukiliya_Salehi
Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran, Ali Akbar Salehi, ya bayyana cewa, ba za a sake cimma wata sasantawa game da yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma tsakanin manyan kasashen duniya.
Mista Salehi wanda ya bayyana hakan jiya a birnin Rome, na kasar Italiya, ya ce, kasarsa ta sha nanata cewa, bakin alkalami ya riga ya bushe game da wannan yarjejeniya da ka cimma a cikin shekara 2015.
Dama kafin hakan ministan harkokin wajen kasar ta Iran Mohammad Javad Zarif ya yi gargadin cewa, Tehran za ta martaba tanade-tanaden dake cikin yarjejeniyar ce idan har ragowar bangarorin da wannan batu ya shafa suka martaba ta.
Takadamma ta kunno kai kan yarjejeniyar ce tun bayan da Amurka ta yi barazanar fucewa daga cikinta, bisa zargin Iran da saba mata, duk da cewa hukumar makamashin nukiliya ta Duniya ta ce Iran din na mutuntunta yarjejeniyar.