Limamin Juma'ar Tehran: Amurka Ta Gama Karya Yejejeniyar Nukiliya
Ayatullah Ahmad Khatami waanda yake magana akan matsayar Amurka danagne da yarjejeniyar Nukiliyar, ya ce; Babu wani abu da ya saura da Amurkan ba ta take ba.
Limamin na Tehran ya ci gaba da cewa; A lokuta da dama jami'an gwamnatin Iran sun sha bayyana cewa; Babu fagen sake kulla wata sabuwar yarjejeniyar ta Nukiliya, wanda hakan shi ne daidai.
Har ila yau, limamin juma'ar ya yi ishara da yadda kasashen Turai suke goyon bayan ci gaba da aiki da yarjejeniyar, sannan ya kara da cewa; Idan har turawan za su fuskanci zabi tsakanin mu'amala da Iran ko Amurka za su zabi Amurka ne.
A cikin kwanakin bayan nan, Amurka tana yin magana akan yarjejeniyar Nukiliyar Iran tare da kokarin sauya ta, ko yin watsi da ita.