Amano: Iran Na Ci Gaba Da Aiwatar Da Yarjejeniyar Nukiliya
Babban sakataren hukumar kasa da kasa ta Makamashin Nukiliya ya ci gaba da cewa; Shekaru biyu bayan yarjejeniyar Nukiliyar Iran tana ci gaba da aiki da ita.
Yokiya Amano wanda ya gabatar da jawabi a wurin bikin cikar hukumar shekaru sittin da fara aiki wanda aka bude a birnin Washington na kasar Amurka, ya ci gaba da cewa: Shirin Nukiliyar Iran yana karkashin tsarin sanya ido mafi tsauri da hukumar take da shi, kuma kasar ta Iran tana aiki da dokokin yarejeniyar hana yaduwar makaman Nukiliya.
Har ila yau, Amano ya ce; Bisa radin kanta Iran din ta bai wa hukumar damar isa ga wasu cibiyoyin nata domin gudanar da bincike.
An cimma yarjejeniyar Nukiliyar ne a tsakanin Iran da kasashe biyar masu dawwamammun kujeru a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da kuma karin kasar Jamus a 2016.