Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Zata Kara Karfafa Alakarta Da Kasashen Nahiyar Afrika
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i2551-jamhuriyar_musulunci_ta_iran_zata_kara_karfafa_alakarta_da_kasashen_nahiyar_afrika
Mataimakin ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran a bangaren hudda da kasashen Larabawa da nahiyar Afrika ya jaddada aniyar kasar Iran na bunkasa alakarta da kasashen Afrika.
(last modified 2018-08-22T06:57:59+00:00 )
Mar 17, 2016 02:11 UTC
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Zata Kara Karfafa Alakarta Da Kasashen Nahiyar Afrika

Mataimakin ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran a bangaren hudda da kasashen Larabawa da nahiyar Afrika ya jaddada aniyar kasar Iran na bunkasa alakarta da kasashen Afrika.

A ganawarsa da jakadun kasashen nahiyar Afrika a birnin Tehran a jiya Laraba; Mataimakin ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran a bangaren hudda da kasashen Larabawa da na Afrika Husain Amir Abdul-Ilahiyon ya jaddada aniyar kasar Iran ta bunkasa alakarta da kasashen nahiyar Afrika tare da bude wani sabon shafi a fagen habaka alakar kasuwanci da tattalin arziki a cikin shekaru biyar masu zuwa.

Amir Abdul-Ilahiyon ya kara da cewa; Dage takunkumin karya tattalin arziki kan kasar Iran wani babban dama ne ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran a fagen bunkasa alakarta da kasashen duniya musamman kasashen nahiyar Afrika.