IAEA : Iran Ta Rike Amana_ Yukiya Amano
(last modified Thu, 23 Nov 2017 17:28:45 GMT )
Nov 23, 2017 17:28 UTC
  • IAEA : Iran Ta Rike Amana_ Yukiya Amano

Babban daraktan hukumar yaki da yaduwar makamman nukiliya ta duniya (IAEA), ya ce Jamhuriya musulinci ta Iran ta rike amana kan yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da ita a 2015.

Yukiya Amano, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka karanto a taron gwamnoni na hukumar, inda ya ce Iran na ci gaba da mutunta yarjejeniyar.

Mista Amano ya kuma yi bayyani akan ziyara da ya kai zuwa Iran, inda ya ce ya kara jinjinawa Iran akan haske da hadin kan da take bayarwa akan yarjejeniyar da aka cimma da ita.

Hukumar ta (IAEA) ta ce tana ci gaba da binciken dukkan cibiyoyin Iran, kamar yadda yarjejeniyar ta tanada, ciki har da wurare da wasu na'u'rori , amma kawo yanzu hukumar ta samu shiga dukkan wuraren da ta bukaci shiga.