Kakakin Majalisar Iran: Manzon Allah Ne Rukunin Hadin Kan Musulmi
(last modified Wed, 29 Nov 2017 12:09:08 GMT )
Nov 29, 2017 12:09 UTC
  • Kakakin Majalisar Iran: Manzon Allah Ne Rukunin Hadin Kan Musulmi

Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Dr. Ali Larijani wanda yake magana a lokacin bukukuwan Mauludin annabi (s.a.w.a) ya yi wa dukkanin al'ummar musulmi murnar zagayowar wannan rana ta haihuwar ma'aikin Allah.

Dr. Larijani ya kara da cewa; Idan ace musulmi za su yi aiki da koyarwar da manzon Allah (s.a.w.a) ya zo musu da ita,  to da yanayin da musulmi suke ciki a wannan lokacin ya fi haka, ta yadda a yanzu adadinsu ya haura biliyan daya, amma kuma  sun rusuna a gaban manyan kasashen duniya.

A nan Iran ana fara bikukuwan Mauludin annabi daga ranar 12 ga watan Rabi'ul Auwali zuwa 17 gare shi a matsayin makon hadin kai, kamar yadda Imam Khumaini ya ayyana.

Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya yi ishara da yadda manyan kasashe suke son yin iko akan al'ummar musulmi ta hanyoyi da dama da suka hada da kirkiro kungiyoyin yan ta'adda domin  musulmi su rika zubar da jininsu da kansu